ABNA24 : Majiyar dakarun ta kara da cewa a lokacin dawowansu daga aikin hana sulalenwar sai motarsu ta taka nakiya wacce mayakan na Daesh su ka dasa a kan hanya wanda kuma yayi sanadiyyar shahadar mutum guda.
Kafin haka dai dakarun Hashdu ne suke gadin dogayen sandunan wayoyin wutan lantarki a kasar wadanda kungiyar ta Daesh ta dade ta na lalata su. Kamar yadda ta yi a lardunan Diala da kuma Ninawa. A halin yanzu dai dakarun Hasdu su ne ginshikin tsaron kasar Iraki, sannan masu tallafawa sojojin da sauran Jami’an tsaron kasar ta Iraki.
342/